Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, wata babbar cibiyar kula da harkokin musulmi ta kasar Rasha ta shirya gudanar da wata gasar karatun kur'ani mai tsarki a birnin Moscow fadar mulkin kasar. Bayanin ya ci gaba da cewa wannan daya ne daga cikin muhimman taruka da wannan cibiya ke shirya gudanarwa a sassa daban-daban na kasar, da nufin kara karfafa gwiwar musulmin kasar wajen ci gaba da bada himma a harkokin addini. 561198