IQNA

Suriya Ta Bukaci Maida Martani Mai Karfi Kan Tilastawa Palasdina Yin Hijira

15:46 - April 14, 2010
Lambar Labari: 1907314
Bangaren siyasa da zamantakewa;Bashar Asad shugaban kasar Suriya a ranar ashirin da uku ne a wata ganawa da babban sakataren kungiyar larabawa a birnin Damaskos ya bukaci maida marati mai karfi cikin gaggawa kan yadda haramtacciyar kasar isra'ila ta bullo da wani sabon tsari na tilastawa Palasdinawa yin gudun hijira.
Daga kasar Suriya ne cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna bayan ta nakalto daga majiyar gwamnatin kasar suriya Sana ta watsa rahoton cewa; Bashar Asad shugaban kasar Suriya a ranar ashirin da uku ne a wata ganawa da babban sakataren kungiyar larabawa a birnin Damaskos ya bukaci maida marati mai karfi cikin gaggawa kan yadda haramtacciyar kasar isra'ila ta bullo da wani sabon tsari na tilastawa Palasdinawa yin gudun hijira. A wannan ganawa ta Shugaban Bashar Asad da babban sakataren kungiyar hadin kan larabawa Amr Musa ya jaddada masa cewa; kungiyar hadin kan larabawa da kungiyoyin kasa da kasa dole su dauki mataki kakaura kan siyasar baya bayan nan ta haramtacciyar kasar Isra'ila.

562038

captcha