Bangaren ilimi da nazari:cibiyar duniya mai kokarin tabbatar da sulhu ta Musulunci a kwana biyu da ta yi tana gudanar da taronta a Indiya ta bawa Ayatullahi Taskhiri babban sakataren cibiyar duniya ta kara kusanto da musulmi da kuma malama Shila Dikshit waziriyar lardin Dehli Kyautar tabbatar da sulhu na adalci.
Daga hukumar da ke kula da yada al'adun Iran a ketare ,cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan Iran Ikna ta watsa rahoton cewa; cibiyar duniya mai kokarin tabbatar da sulhu ta Musulunci a kwana biyu da ta yi tana gudanar da taronta a Indiya ta bawa Ayatullahi Taskhiri babban sakataren cibiyar duniya ta kara kusanto da musulmi da kuma malama Shila Dikshit waziriyar lardin Dehli Kyautar tabbatar da sulhu na adalci.A cikin kwanaki biyu da aka yi ana gudanar da wannan taro an yi nazari da bincike kan yadda ake kokarin tabbatar da sulhu mai inganci a duniya da kuma irin matsalolin da ake fuskanta.
561942