IQNA

Karamar Jami'a Ta Bada Ilmin Hadisi Tamkar Madogara Ce Ta Duniyar Musulmi

Bangaren ilimi da nazari: ministan harkokin addini a kasar Aljeriya ya bayyana cewa; kafa karamar jami'a da za rika ilmantar da hadisai da mu'assisar Darul Hadis da irin ayyukan da suke aiwatar da yadda suke da fawa wata madogara ce babba ga duniyar musulmi da Iran.
Daga mu'assisar ilimi da al'adu a darul Hadis ne cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ta watsa rahoton cewa; : ministan harkokin addini a kasar Aljeriya ya bayyana cewa; kafa karamar jami'a da za rika ilmantar da hadisai da mu'assisar Darul Hadis da irin ayyukan da suke aiwatar da yadda suke da fawa wata madogara ce babba ga duniyar musulmi da Iran.Bu Abdallah Gulamullah a marecen ranar litinin ashirin ga watan Farvardin shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara a bayan ya kammala ziyarta Darul Hadis na birnin Qum a wata tattaunawa da manema labari ya yi wannan bayani.


561915