Bangaren al'adu da Fasaha:A kasar Spain ne za a gudanar da bincike kan bangaren ilimi da mahanga da halayansa da kuma tasirin Sa'adi a duniya a matsayinsa na mia hikima kuma mawaki dan Iran kuma wannan za a gudanar ne a daidai lokacin tunawa da zagayowar ranar mutuwarsa a ranar biyu ga watan Ordebehesht.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran daga reshenta da ke hukumar da ke kula da yada al'adun kasar Iran a Ketare da kuma kusanci a tsakanin musulmi ta watsa rahoton cewa; A kasar Spain ne za a gudanar da bincike kan bangaren ilimi da mahanga da halayansa da kuma tasirin Sa'adi a duniya a matsayinsa na mia hikima kuma mawaki dan Iran kuma wannan za a gudanar ne a daidai lokacin tunawa da zagayowar ranar mutuwarsa a ranar biyu ga watan Ordebehesht. Kuma jami'ar Alikanta a kasar Spain tare da hadin guiwar ofishin yada al'adun Iran a kasar Spain suka shirya wannan taron.
561919