Kamfanin dilalncin labaran iqna ya nakalto daga jaridar kasar Bahrain cewa, wata kotu a kasar Bahrain ta hukunta muyumin nan dan kasar wanda ya wulaknata kur'ani mai tsarki a kwanakin baya, wanda zai kwashe tsawon shekaru a gidan kaso. Bayanin ya ci gaba da cewa mutumin ya jefa wata safha daga cikin kur'ani mai tsarki a cikin kwandon shara da nufin wulakata kur'ani a matsayinsa na musulmi, lamarin da ya fusata musulmin kasar bayan samun labarin abin da ya aikata na mummunan aiki.561871