IQNA

Limaman Masallatai Na Samu Horo A Kasar Bahrain

19:47 - April 14, 2010
Lambar Labari: 1907387
Bangaren kasa da kasa; Limaman masallatai a kasar Bahrain gami da masi sar da sakon addini ga al'umma suna samun wani horo na musamman domin wayar da kan al'ummar kasar.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga jaridar kasar Bahrain an habarta cewa, Limaman masallatai a kasar Bahrain gami da masi sar da sakon addini ga al'umma suna samun wani horo na musamman domin wayar da kan al'ummar kasar a dukkanin sassa, musamman a bangarori na rayuwar zamantakewar jama'a. Bayanin ya kara da cewa wannan na daya daga cikin muhimman ayyuka da ma'aikatar kula da harkokin addini ta kasar kan shirya gudanarwa.561923


captcha