IQNA

Yahudawa Na Kafa Hujja Da Kur'ani Domin Yahudantar Da Qods

11:14 - April 15, 2010
Lambar Labari: 1907460
Bangaren kasa da kasa; Wasu kungiyoyin yahudawan sahyuniya na yin amfani da ayoyin kur'ani mai tsarki wajen kafa hujjar cewa birnin Qods mallakin yahudawa ne a tsawon tarihin duniya.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga jaridar kasar Kuwait ta Al-ra'ayi an bayyana cewa, wasu daga cikin kungiyoyin yahudawan sahyuniya na yin amfani da ayoyin kur'ani mai tsarki wajen kafa hujjar cewa birnin Qods mallakin yahudawa ne a tsawon tarihin duniya.Bayanin ya kara da cewa babbar manufar wannan aiki ita ce kara birkita tunanin masu kallon lamarin da hakikanin surarsa ta zaluncin yahudawa a tsakanin al'ummomin musulmi da sauran al'ummomin duniya. 562518



captcha