Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, wani labari da ya fito daga majiyar kungiyar hadin kan kasashen musulmi ya tabbatar da cewa, an zabi kasar Yeman a matsayin mai taimaka ma kasar da ke jagoranci kungiyar hadin kan kasashen musulmi a zagaye na talatin da bakwai. Bayanin ya ci gaba da cewa kasar Yeman za ta taka rawa a matsayinta na mai taimaka ma shugaban zagaye-zagaye na wannan kungiya a matsayinta na kasar da take da cikakkiyar masaniya kan harkokin musulmi.562493