Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Kungiyar raya al'adu da ilimin addinin musulunci ta jaddada muhimmancin kara fadada harkar tarbiya a cikin cibiyoyi da makarantun musulunci da ke kasashen musulmi, da ma sauran kasashen duniya. Bayanin ya ci gaba da cewa wannan zai taimaka matuka wajen samar da malamai masu ilimi da tarbiya irin ta addinin musulunci a cikin kasashen musulmi, wanda kuma ba zai samu ba sai ta hanyar bada muhimmanci a makarantu da cibiyoyin addini. 562672