Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto wani bayani daga wani shafin yanar gizo da ke cewa, za a gudanar da wani zaman taro da zai bahasi kan muhimman mas'aloli da addinin musulunci ya bayyana mahangarsa a kansu a bangarorin zamantakewar jama'a, wanda za a gudanar a babbar jami'ar nan ta oxford da ke birnin London na kasar Birtaniya. Bayanin ya ci gaba da cewa a kan shirya taruka daban-daban a wannan jami'a da ke kara bayar da haske kan lamurran da dama da musulunci ya bayyana m,ahangarsa a kansu. 562703