IQNA

An Fara Buga Mujalla Kan Harkokin Bankin Musulunci A Kuwait

11:14 - April 15, 2010
Lambar Labari: 1907466
Bangaren kasa da kasa; An fara buga wata mujalla dangane harkokin bankin musulunci a kasar Kuwait, wadda za ta rika yin karin haske dangane da harkokin kudi a mahangar musulunci.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labarai da ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran kasar Kuwait cewa, An fara buga wata mujalla dangane harkokin bankin musulunci a kasar Kuwait, wadda za ta rika yin karin haske dangane da harkokin kudi a mahangar musulunci. Bayanin ya ci gaba da cewa za a yi amfani da wannan mujalla wajen bayyana matsayin musulunci kan yadda ake ajiyar kudi a bankunan musulunci da kuma saka hannayen jari. 562731



captcha