IQNA

Karfafa Imani Da Hadin Kai Sun Zama Wajibi A Tsarin Musulunci

11:14 - April 15, 2010
Lambar Labari: 1907467
Bangaren siyasa; Daya daga cikin mambobin kwamitin tsaron kasa a majalisar shawara ta kasar Iran ya bayyana cewa hadin kai da karfafa imani sun zama wajibi a karkashin tsarin musulunci.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, bangaren hulda da jama da kuma yada labarai na kwamitin tsaron kasa ya bayyana cewa, daya daga cikin mambobin kwamitin tsaron kasa a majalisar shawara ta kasar Iran ya bayyana cewa hadin kai da karfafa imani sun zama wajibi a karkashin tsarin musulunci. Sayyid Husseini ya bayyana cewa dole a mayar da hankali wajen fadakar da mutane a dukkanin bangarori na karfafa imani da Allah madaukakin sarki, domin ta hakan ne kawai za a iya samun tsayuwa wajen kare manufofi na addini. 562802


captcha