IQNA

Gasar Al'adu Musamman A Ranekun Haifuwar Hadarat Zainab (S) A Malaishiya

Bangaren al'adu da fasaha:ofishin da ke kula da yada al'adun Iran a kasar Malaishiya ne ya dauki nauyin gudanar da wannan gasar ta musamman a lokacin zagayowar ranekun Haifuwar Hadarat Zainab (S).
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan Jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna daga reshenta daga hukumar kula da yada al'adun Iran da kuma kara kusanci a tsakanin musulmi ta watsa rahoton cewa; ofishin da ke kula da yada al'adun Iran a kasar Malaishiya ne ya dauki nauyin gudanar da wannan gasar ta musamman a lokacin zagayowar ranekun Haifuwar Hadarat Zainab (S). Kuma wannan gasar ta kumshi tambaya da amsa kan abubuwan tarihi da suka shafi rayuwar wannan baiwar Allah Hadarat Zainab (S).



562399