Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin yanar gizo na Hjjat cewa, za a gudanar da taron maulidin Sayyida Zainab(SA) a birnin London na kasar Birtaniya, wanda babbar cibiyar da harkokin addinin musulunci ta kasar ta shirya gudanarwa. Bayanin ya ci gaba da cewa taron wanda za agudanar zai mayar da hankali kan muhimman lamurran da ya kamata a mayar da hankali a kansu dangane da darussan da ke cikin rayuwar sayyida Zainab day a kamata a yi koyi da su a cikin rayuwarmu ta yanzu.564458