Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, kamfanin dillancin labaran rasid na kasar Saudiyya ya habarta cewa, Daya daga cikin fitattun malaman addini na kasar Saudiyya kuma limamin juma'a a yankin Katif na mabiyar tafarkin iayalan gidan manzon Allah Abbas Sa'id, ya kirayi mahukuntan kasar da su amince da banbancin mazhabobin addinin musulunci. Bayanin ya ci gaba da cewa kiran na malamin ya zo a daidai lokacin da ake kiran malaman mahukuntan kasar ta Saudiyya da su amince da banbancin mazhabobin addini, tare da kiyaye hakkokin kowane bangare. 564334