Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a cikin wata zantawa da ta hada shugaban majalisar dokokin Iran da mataimakin shugaban majalisar dokokin Pakistan ya bayayna cewa, Alummar kasar Pakistan ta yi Allawadai da ayyukan ta'addancin da haramtacciyar kasar Isra'ila kan al'ummar palastinu a birnin Qods mai alfarma. Bayanin ya ci gaba da cewa wanann mataki ne da ke tababtar da cewa al'ummomin duniya na ci gaba da kara fadaka kan bakaken manufofin gwamnatin yahudawa. 564128