Bangaren manema labarai/Ali Huseini Qumi: A masallacin Imam Husein (AS) a lardin Sheikh Nashin na birnin Dubai ne za a gudanar da taron bukukuwan zagayowar irin wannan rana da aka haifi Hadarat zainab (S).
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna a hadeddiyar daular larabawa ta watsa rahoton cewa; Ali Huseini Qumi: A masallacin Imam Husein (AS) a lardin Sheikh Nashin na birnin Dubai ne za a gudanar da taron bukukuwan zagayowar irin wannan rana da aka haifi Hadarat zainab (S). Har ila yau a daidai wannan lokaci na zagayowar haifuwar Akila bani Hashim Hadarat Zainab Kubra (S) za a gudanar da bukukuwar murna a garuruwa daban daban a hadeddiyar daular larabawa. Bugu da kari Masallacin Imam Husein (AS) dake birnin Dubai na hadeddiyar daular Larabawa shi ma zai karbi bakuncin masoya ahlul Baiti da imamai da gudanar da wannan buki a ranar talatin ga watan Farvardin na shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da takwas hijira shamsiya bayan sallar magariba.
564421