Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da ya nakalto daga jaridar kasar Libya ta Fajr jaded an bayyana cewa, a daidai lokacin da ake shirin fara gudanar da gasar karatun kur'ani da harda gami da tajwidi a kasar Libya, matasa da dalibai na ta yin kokari a wannan bangare. Bayanin ya ci gaba da cewa rahoton da jaridar ta yada ya yi nuni da irin yadda dalibai musamman ma na makarantun sakandare suke ta fadi tashin ganin sun samu shiga cikin wannan gasa, inda suke mayar da hanakali wajen hardar kur'ani da kuma tajwidi. 564902