Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, kamfanin dillancin labaran Muhit ya habarta a cikin shafinsa na yanar gizo cewa, Ana ci gaba da gudanar da wani taro na bayar da horo kan koyarwar sauran addinai a kasar Faransa, da nufin samara da daidaito wajen fahimtar juna tsakanin mabiya addinai. Bayanin ya ci gaba da cewa, yanzu haka dai taron na samun halartar wakilai daga kungiyoyin addinai daban-daban na kasar Faransa da ma wasu kasashen ketare. 564812