IQNA

Fara Zaman Taron Kwamitin Kula Da Harkokin Mata Na ISESCO

11:34 - April 21, 2010
Lambar Labari: 1910604
Bangaren kasa da kasa; An fara gudanar da zaman kwamitin kula da harkokin mata na kungiyar raya ilimi da la'adun kasashen musulmi ta ISESCO.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani bayani da ya nakalto daga wani shafin yanar gizo na yada labaran kasashen musulmi an habarta cewa, an fara gudanar da zaman kwamitin kula da harkokin mata na kungiyar raya ilimi da la'adun kasashen musulmi ta ISESCO, wanda ke samun halartar mambobin kwamitin. Bayanin ya ci gaba da cewa yanzu haka ana ci gaba da gudanar da zaman taron a babban dakin taro na kungiyar. A lokacin da yake bude zaman taron babban sakataren kungiyar Abdulaziz Usman Tuwaijari ya jadda muhimmancin gudanar da taron. 565546




captcha