Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, jaridar kasar Qatar ta sharq ta habarta cewa, shugaban bangaren cibiyar kula da harkokin a'adu da ilimi ta kasar Iran a reshenta na kasar Qatar, zai bude wani taron baje kolin rubutun kur'ani mai tsarki da kyakkyawan rubutun Iraniyawa a birnin Doha na kasar Qatar, wanda zai samun halartar wakilan cibiyoyin kur'ani. Bayanin ya ci gaba da cewa yanzu haka an fara gudanar da dukkanin shirye-shiryen da suka kamata na gudanar da baje kolin. Haka nan kuma ya kara da cewa wasu daga cibiyoyin muslunci na kasar musamman ma harkokin kur'ani za su halarci baje kolin. 565587