Bangaren kasa da kasa: Bradford dan kasar Britaniya ne ya lashe gasar zana mafi kyauwon Hasumiya ta masallaci a nahiyar Turai.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna bayan ta nakalto daga majiyar labarai ta kamfanin dillancin labarai na gwamnatin Faransa AFP ta watsa rahoton cewa; Bradford dan kasar Britaniya ne ya lashe gasar zana mafi kyauwon Hasumiya ta masallaci a nahiyar Turai.
A ranar talatar da ta gabata talatin da daya ga watan farvardin na shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara aka gudanar da bukin girmamawa a zauren majalisar Turai da ke birnin Istrasburg na kasar Faransa kuma tawagar alkalai sun yi baki daya wajen bayyana ra'ayin cewa masallacin garin Bordeau na kasar Faransa mai hasumiya hudu shi ne yafi kyau daga cikin sauran makamantansu a Turai.
566366