IQNA

Musulunci A Nahiyar Afrika Na saurin Yaduwa

14:26 - April 22, 2010
Lambar Labari: 1911066
Bangaren kasa da kasa: mu'assisar bincike ta The Pew Research Center da ked a matsugunninta a birnin Washinton na kasar Amerika ce ta watsa wani rahoto kan yadda Musulunci ke yaduwa a nahiyar Afrika inda ta gano cewa Musulunci na saurin yaduwa a nahiyar Afrika musamman ta bakar fata a kuduncin sahara.
Cibiyar da ke kula da harkokin Kur'ani a nan Jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna bayan ta nakalto daga ucide ta watsa rahoton cewa: mu'assisar bincike ta The Pew Research Center da ked a matsugunninta a birnin Washinton na kasar Amerika ce ta watsa wani rahoto kan yadda Musulunci ke yaduwa a nahiyar Afrika inda ta gano cewa Musulunci na saurin yaduwa a nahiyar Afrika musamman ta bakar fata a kuduncin sahara. Sakamakon wannan bincike da jin ra'ayin jama'a na wannan mu'assisar bincike ya fara net un watan Satumban shekara ta dubu biyu da takwas zuwa watan Afrilul shekara ta dubu biyu da goma da kuma aka gudanar a kasashe goma sha tara na Afrika da aka samu karuwar yawan musulmi a cikin wadannan shekaru.

566411

captcha