IQNA

Za A Gudanar Da Taro Kan Faransa Da Musulunci

14:29 - April 24, 2010
Lambar Labari: 1911834
Bangaren kasa da kasa: Taro mai taken Faransa Da Musulunci da hadin guiwar kungiyar matasan Faransa suka shirya a yau asabar hudu ga watan Ordebehesh na wannan shekara ta hijira Shamsiyar ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara kuma za a gudanr da wannan taro a birnin Rhone na kasar ta Faransa.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan Jamhuriyar Musulunci ta Iran ikna bayan ta nakalto daga umma-unitrd ta matasan wannan kasa ta Faransa ta watsa rahoton cewa; Taro mai taken Faransa Da Musulunci da hadin guiwar kungiyar matasan Faransa suka shirya a yau asabar hudu ga watan Ordebehesh na wannan shekara ta hijira Shamsiyar ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara kuma za a gudanr da wannan taro a birnin Rhone na kasar ta Faransa. Wannan taro zai bada damar fayyace biri har wutsiya musamman idan aka yi la'akari da yadda gwamnatin Faransa a yan kwanakin nan ke ci gaba da matsa lamba kan takurawa musulmi da ke rayuwa a wannan kasa da nuna masu karan tsana da takurawa.

567019
captcha