IQNA

A Paris Ne Za A Gudanar Da Zangon Horo Na Tattalin arzikin Musulunci

14:29 - April 24, 2010
Lambar Labari: 1911840
Bangaren kasa da kasa: a birnin Paris Fadar mulkin kasar Faransa ne za a gudanar da taron bada horo kan tsarin tattalin arziki irin na Musulunci a wannan kasa da hadin guiwar ci gaban tattalin arziki da kudi na faransa AIDIMM ta shirtya a ranar asabar takwas ga watan Hurdad na wannan shekara.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna bayan ta nakalto daga AIDIMM ta watsa rahoton cewa: a birnin Paris Fadar mulkin kasar Faransa ne za a gudanar da taron bada horo kan tsarin tattalin arziki irin na Musulunci a wannan kasa da hadin guiwar ci gaban tattalin arziki da kudi na faransa AIDIMM ta shirtya a ranar asabar takwas ga watan Hurdad na wannan shekara. A wajen wannan taro za a yi nazari kan mahangar Musulunci da tsarin banki a Musulunci da kuma za a kwatamta shi da tsarin bankoki da ake da su a yau a duniya domin yin nazarin irin ci gaba da kuma wane yafi dacewa a bi domin kaucewa fadawa irin matsalolin tattalin arziki da ke fuskantar duniya a yau.

567030
captcha