IQNA

Musulmin Kuduncin Faransa Za Su Gudanar Da Babban Taro A tsakaninsu

Bangaren kasa da kasa" musulmin kuduncin faransa Rams za su gudanar da babban taro karo na takwas a ranar biyu ga watan Khurdad na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara kuma za su gudanar da wannan taro ne a birnin Marseil na kasar Ta Faransa.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan Jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna bayan ta nakalto daga shafin Internet na www.r-a-m-s.net ya watsa rahoton cewa; " musulmin kuduncin faransa Rams za su gudanar da babban taro karo na takwas a ranar biyu ga watan Khurdad na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara kuma za su gudanar da wannan taro ne a birnin Marseil na kasar Ta Faransa. A wajen wannan taro da aka bawa taken ma'anawiyat,yanayi ,yan uwantaka da hulda ta bai daya za a tattaunawa irin matsalolin da musulmi ke fuskanta a tsakaninsu da kuma sauran matsaloli da suke fuskanta tare da sauran abukan zama da kuma yin nazarin hanyoyin bi wajen magance irin wadannan matsaloli da kuma masanyar ra'ayi.

567037