Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran ikna bayan ta nakalto daga jaridar kasar saudiya Alwatan ta watsa rahoton cewa: ma'aikatar shari'a a kasar Holand a jiya ne hudu ga watan Ordebehesh na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara a hukumce ta yi watsi da bukatar limaman masallatai da wakilan cibiyoyin musulmi a wannan kasa na kafa Kotun Musulunci . Su dai wadanda suka gabatar da wannan bukata sun nemi kafa kotu da za ta yi aiki da dokokin Musulunci ga musulmin wannan kasa amma ministan da ke kula da harkokin shari a awanann kasa ya yi watsi da wannan bukata a kasar da ke ikirarin yancin fadin albarkacin baki da yancin kowa da kowa.
568068