IQNA

An Fara Gasar Karatun Kur'ani Na Tartili A Imarat

16:13 - April 26, 2010
Lambar Labari: 1913194
Bangaren kasa da kasa; a hadeddiyar daular larabawa ne aka fara zangon farko na gasar karatun Kur'ani na Tartili da ake yi wa lakabi da kyautar Dubai kuma an fara wannan gasar ne a ranar hudu da watan ordebehesh na shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna bayan ta nakalto daga jaridar Alkhalij da ke fitowa a hadeddiyar daular larabawa ta watsa rahoton cewa; a hadeddiyar daular larabawa ne aka fara zangon farko na gasar karatun Kur'ani na Tartili da ake yi wa lakabi da kyautar Dubai kuma an fara wannan gasar ne a ranar hudu da watan ordebehesh na shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara hijira shamsiya. Ibrahim Muhammad Bunlaha shugaban komitin shirya wannan gasa ta Dubai ya bayyana cewa: a wannan gasa yan takara dari hudu da arba'in da daya ne za su fafata da juna day a hada dukan bangarori na matasa,yara da limaman masallatai da ladanai.

567977

captcha