IQNA

A Bude Baje Koli Na Dindindim Na Fasahar Musulunci A Dirtrawit Na Amerika

Bangaren kasa da kasa; a Dritrawit na kasar Amerika ne aka bude baje koli na dindindim na fasahar Musulunci.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna bayan ta nakalto daga jaridar kasar Koweiti Alkabas ta watsa rahoton cewa; ; a Dritrawit na kasar Amerika ne aka bude baje koli na dindindim na fasahar Musulunci. A wajen wannan kasuwar baje koli da aka gudanar a gidan ajiyar kayayyaki na garin Dirtrawit na Amerika zai zama na dindindim kuma an nuna wani bangare na kur'ani a karni na goma sha biyar miladi da kuma wasu kayayyakin fasaha da kayan hannu na musulmi a lokuta daban daban da aka nunawa jama'a.



568775