Bangaren kasa da kasa: Uwaye musulmi na bukatar sa ido kan kafafen watsa labarai da yayansu kanana za su kalla idan suna son su samu tarbiya ta gari da gare yayansu a nan gaba.
Emiliya TakiyiYuva yar jarida kuma mukaddashin shugaban komitin Mata a jam'iyar musulmi a jamhuriyar azarbeijan a bayan kammala taron musulmi masana a da hukumar da ke kula da al'adu da dangantaka ta Musulunci ta bayyana cewa: Uwaye musulmi na bukatar sa ido kan kafafen watsa labarai da yayansu kanana za su kalla idan suna son su samu tarbiya ta gari da gare yayansu a nan gaba. Har ila yau ta yi kira ga uwaye da su fahimci irin hadarin da ke tattare da irin kafafen watsa labarai na yammacin Turai da wasu a aksashenmu da ke watsa shirye-shirye ba tare da kiyaye wasu abubuwa da kan iya zama hadari ga tarbiyar yara kanana a yanzu da kuma nan gaba.
568506