IQNA

Fara taron Share Fage Kan Harkokin Yara A Duniyar Musulmi

Bangaren kasa da kasa; ministoci da ke kula da harkokin yara kanana a duniyar musulmi sun fara gudanar da taron share fage kan harkokin yara kanana a duniya musulmi daga yau sha uku ga watan ordebehesht na shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara a birnin Trablus fadar mulkin kasar Libya kuma za a kwashe kwanaki biyu ana gudanar da wannan taro.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci tai ran Ikna bayan ta nakalto daga majiyar watsa labarai ta Muhit ta watsa rahoton cewa; ministoci da ke kula da harkokin yara kanana a duniyar musulmi sun fara gudanar da taron share fage kan harkokin yara kanana a duniya musulmi daga yau sha uku ga watan ordebehesht na shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara a birnin Trablus fadar mulkin kasar Libya kuma za a kwashe kwanaki biyu ana gudanar da wannan taro. Mahalarta wannan taro za su tattauna matsalolin da yara kanana ke fuskanta a duniyar musulmi da kuma hanyoyin da za su magance matsalolin da inganta rayuwarsu cikin sauki su rayu.

572759