Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna bayan ta nakalto daga jaridar da ke fitowa a Hadeddiyar daular larabawa Alkhalij ta watsa rahoton cewa: mahalarat taron kasa da kasa kan fassarar kur'ani kan ayoyi masu magana kan abu guda sun bada shawarar kafa cibiyar fassarar kur'ani a hadeddiyar daular larabawa.
Mahalarta wannan taro sun bayar da wannan shawara ce da suke ganin yin aiki da ita zai taimaka matuka gaya wajen magance irin matsalolin da wannan bangare na tafsirin kur'ani ke fuskanta a duniyar musulmi.
574171