Bangaren kasa da kasa; Hukumar da ke al'adun Musulunci ta Asesko tare da hadin guiwar kungiyar da ke kula da yada Musulunci a kasashen duniya daga ranar ashirin da daya ga watan Ordebehesht zuwa ashirin da uku ga watan a wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara sun shirya wani zangon bada horo ga masu tabligin yada addinin Musulunci da limaman masallatai a Afrika kuma wannan horo za a gudanar da shi ne a birnin Abijan babban birnin kasuwancin kasar Cote D'ivoire.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna bayan ta nakalto daga majiyar labarai ta Muhit ta watsa rahoton cewa; Hukumar da ke al'adun Musulunci ta Asesko tare da hadin guiwar kungiyar da ke kula da yada Musulunci a kasashen duniya daga ranar ashirin da daya ga watan Ordebehesht zuwa ashirin da uku ga watan a wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara sun shirya wani zangon bada horo ga masu tabligin yada addinin Musulunci da limaman masallatai a Afrika kuma wannan horo za a gudanar da shi ne a birnin Abijan babban birnin kasuwancin kasar Cote D'ivoire. Za a samu halartar wakilai daga kasashen mauritaniya,Senegal.Mali.Guine Konakri,Benin,Burkina Faso,Togo,Niger,Chadi da Cote D'ivoire.
575029