Bangaren kasa da kasa; a kasar Koweiti ne za a gudanar da taron kasa da kasa da bincike kan al'adun Musulunci da tattaunawa daga ranar ashirin da daya zuwa ashirin da biyu ga watan Ordebehesht na shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna bayan ta nakalto daga majiyar watsa labarai ta Muhit ta watsa labarin cewa a kasar Koweiti ne za a gudanar da taron kasa da kasa da bincike kan al'adun Musulunci da tattaunawa daga ranar ashirin da daya zuwa ashirin da biyu ga watan Ordebehesht na shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara.wannan taro hukumar da ke kula da al'adun Musulunci tare da hadin guiwar komitin bada taimako na Musulunci a cikin kasashen duniya suka shirya.
574998