Bangaren kasa da kasa: Ofishin Ayatullahi Uzma Said Ali Sistani babban Matrji'in yan Shi'a a birnin Najaf Ashraf ya fitar da wata sanarwa mai cewa walafawa da watsa littafin fikihu Manaf Albagadadi wani cin mutunci ne ga wannan marja'I kuma babu wata dangantaka tsakanin wannan littafi da Ayatullahi Sistani.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan jmahuriyar Musulunci ta Iran Ikna bayan ta nakalto daga majiyar labarai ta Nun ta watsa rahoton cewa; Ofishin Ayatullahi Uzma Said Ali Sistani babban Matrji'in yan Shi'a a birnin Najaf Ashraf ya fitar da wata sanarwa mai cewa walafawa da watsa littafin fikihu Manaf Albagadadi wani cin mutunci ne ga wannan marja'I kuma babu wata dangantaka tsakanin wannan littafi da Ayatullahi Sistani.A yan kwanakin nan an fitar da wani littafi day a shafi Fikihu day a kumshi tambayoyi dubu uku da amsoshinsu da ake danganta su da Ayatullahi Sistani wanda ya wallafa wannan littafi y ace amsoshin da ke cikin littafin sun yi daidai da fatawar Ayatullahi Sistani.
574995