Bangaren kasa da kasa;wasu daga cikin wakilan majalisa a Koweiti sun bada shawarar ayar doka ta kafa mu'assisar da za ta bawa jama'a damar wallafawa da yada kur'anai da hadisan ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayan gidansa da sauran littafai da suka shafi ilmomin kur'ani mai girma.