Bangaren kasa da kasa; Mu'assisar bugawa da watsa littafai ta Darul Khatib a Masar sun rubuta Ayoyin Kur'ani a bisa takardu na musamman da kuma suka baje kolinsu a wajen kasuwar baje kolin littafai ta kasa da kasa da ake gudanarwa a nan birnin Tehran karo na ashirin da uku.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan Jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna daga gurin da ake gudanar da wannan kasuwar baje koli ta littafai a Musalla Imam Komeini ® ta watsa rahoton cewa; Mu'assisar bugawa da watsa littafai ta Darul Khatib a Masar sun rubuta Ayoyin Kur'ani a bisa takardu na musamman da kuma suka baje kolinsu a wajen kasuwar baje kolin littafai ta kasa da kasa da ake gudanarwa a nan birnin Tehran karo na ashirin da uku.A wannan kasuwar baje koli an samu mu'assisoshi da cibiyoyi na ilimi da dama daga cikin Iran da kuma sauran kasashen duniya da suka samu halartar zuwa wajen wannan kasuwar baje koli .
576760