IQNA

Za A Gudanar Da Gasar Kur'ani Da Harda A London

13:34 - May 13, 2010
Lambar Labari: 1922255
Bangaren kasa da kasa: gasar harda da karatun kur'ani a London da cibiyar yada al'adun Iran da Masallacin tsakiyar birnin London suka shirya daga shida zuwa sha biyu ga watan Dai.


Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan Jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna bayan ta nakalto daga iccuk ta watsa rahoton cewa; gasar harda da karatun kur'ani a London da cibiyar yada al'adun Iran da Masallacin tsakiyar birnin London suka shirya daga shida zuwa sha biyu ga watan Dai.Wannan gasar kur'ani ta shafi tajwidi da tilawar Kur'ani kuma masu bukatar halartar wannan gasa suna da zuwa ranar lahadi sha shida ga watan Khurdad na shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara domin rubuta sunayensu yayin da a ranar ashirin da uku ga watan na Khurdad a yi wa wadanda suka rubuta sunayensu tambayoyi kuma wanda ya zo na daya za a gabatar da sunansa a gasar kasa da kasa ta harda da tajwidi da tafsirin kur'ani ta Malik Abdul Aziz na Saudiya da ake gudanar da gasar a Makka.



578539

captcha