Bangaren kasa da kasa: baje kolin kafafen watsa labarai karoi na uku na musulmi za a gudanar da shi daga ranar shida zuwa bakwai ga watan Khurdad na shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara a Kazan babban birnin kasar Tataristan da hadin guiwar kungiyoyin al'adu na musulmi a kasar suka shirya.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna bayan ta nakalto daga info-islam ta watsa rahoton cewa; baje kolin kafafen watsa labarai karoi na uku na musulmi za a gudanar da shi daga ranar shida zuwa bakwai ga watan Khurdad na shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara a Kazan babban birnin kasar Tataristan da hadin guiwar kungiyoyin al'adu na musulmi a kasar suka shirya.Wannan kasuwar baje kolin za a gudanar tare da tuntubar komitin koli na kula da ma'anawiyar musulmi a Tajikistan da burin karawa masu aikin jarida na musulmi a kasar Rasha sanin makamar aiki da yadda rayuwar mutane za ta inganta ta hanyarsu da fadakarwar da kafafen watsa labarai za su yi masu.
578362