Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan Jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna bayan ta nakalto daga majiyar watsa labarai ta techisntan ta watsa rahoton cewa; ; taron saka hannayen jari da kasuwanci na musulmi za a gudanar da shi ne a Kalalanpur babban birnin kasar Malaishiya daga rana sha hudu zuwa sha biyar ga watan Khurdad na shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara.Burin gudanar da wannan taro shi ne fadada dangantakar kasuwanci da saka hannayen jari a tsakanin kasashen musulmi da musulmi sanin salon mai inganci na tafiyar da lamuran da suka shafi tattalin arziki da saka hannayen jari na kasa da kasa da kuma saye da sayarwa tsakanin musulmi da wadanda ba musulmi ba a fadin duniya.
578306