IQNA

Yan Majalisa A Faransa Sun Yi Kashedi Kan Yaduwar Musulunci

13:32 - May 13, 2010
Lambar Labari: 1922266
Bangaren kasa da kasa; Eric Raoult dan majalisa dokokin kasar Faransa daga jam'iyar UMP a ranar talata ashirin da daya ga watan Ordebehsht na shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara a cikin wata wasika day a aikewa shugaban majalisar dokokin Faransa ya bayyana masa fargaba da kashedi kan yaduwa da Musulunci ke yi a kasar.



Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan Jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna bayan ta nakalto daga kamfanin dillancin Labarai na kasar Faransa AFP ta watsa rahoton cewa; ; Eric Raoult dan majalisa dokokin kasar Faransa daga jam'iyar UMP a ranar talata ashirin da daya ga watan Ordebehsht na shekara ta dubu daya da dari uku da tamanin da tara a cikin wata wasika day a aikewa shugaban majalisar dokokin Faransa ya bayyana masa fargaba da kashedi kan yaduwa da Musulunci ke yi a kasar. A cikin wasikar day a aikewa Bernard Accoyer shugaban majalisar dokokin kasar Faransa ya bukace shi da a kafa wani komiti na musamman da zai yi bincike kan yadda Musulunci ke yaduwa a kasar ta faransa da kuma hakan babbar matsala ce ga al'ummar Faransa a cewarsa.



578212

captcha