Bangaren kasa da kasa : mu'assisar kasa da kasa ta Kur'ani ta Dubai tare da hadin guiwar mu'assisar Insan Ta Dubai sun amince da wani shiri na buga kur'ani da harkokin da suka shafi ilimin addinin Musulunci kuma za su buga kur'ani dubu dari uku da tamanin kamar yadda yarjejeniyar da suka sawa hannu ta nuna.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan Jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna bayan ta nakalto daga jaridar hadeddiyar daular larabawa Alkhalij ta watsa rahoton cewa: mu'assisar kasa da kasa ta Kur'ani ta Dubai tare da hadin guiwar mu'assisar Insan Ta Dubai sun amince da wani shiri na buga kur'ani da harkokin da suka shafi ilimin addinin Musulunci kuma za su buga kur'ani dubu dari uku da tamanin kamar yadda yarjejeniyar da suka sawa hannu ta nuna.
578175