Bangaren kasa da kasa; mambobin komitin harkokin addini a majalisar dokokin Masar sun soki Ahmad Aldayib Sheikhul Azahar da Ahmad Nazif firaministan kasar ta Masar kan yadda ba su halarci zaman komitin addini day a yi kan binciken sanin dalilain yin kura-kurai wajen buga Kur'ani mai Girma da kuma bincike kan wadannan kura kurai.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan Jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna bayan ta nakalto daga jaridar kasar masar ta almisriyun ta watsa rahoton cewa; mambobin komitin harkokin addini a majalisar dokokin Masar sun soki Ahmad Aldayib Sheikhul Azahar da Ahmad Nazif firaministan kasar ta Masar kan yadda ba su halarci zaman komitin addini day a yi kan binciken sanin dalilain yin kura-kurai wajen buga Kur'ani mai Girma da kuma bincike kan wadannan kura kurai. Masu sukan Sheikhul Azahar suna gani bai dace ba a ce bai halarci wajen wannna taro ba ganin yadda wannan zama ked a muhimmanci ga jami'ar da ku ya shafi musulmi na duniya ba wai kawai na kasar Masar ba.
579064