Bangaren kasa da kasa; gwamnatin Girka ta yi niyar yiwa wasu masallatai sha hudu na lokacin mulkin Usmaniya a tsibirin Istakoy kwaskwarima.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna bayan ta nakalto daga majiyar haberturk ta watsa rahoton cewa; gwamnatin Girka ta yi niyar yiwa wasu masallatai sha hudu na lokacin mulkin Usmaniya a tsibirin Istakoy kwaskwarima. Wannan mataki da gwamnatin Girka ta yi niyar dauka ya biyo bayan ziyarar da firaministan kasar Turkiya ya kai kasar Girka a wani kokari na kara inganta dangantakar kasashe da gwamnatoci da al'ummomin kasashen biyu ta fuskar siyasa,zamantakewa,tattalin arziki da addini.
579051