Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan Jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna bayan ta nakalto daga majiyar UJM ta watsa rahoton cewa; a Faransa za a gudanar da taro kan dangantakar maza da mata a Musulunci da kungiyar hadin kan matasa musulmi na Faransa UJM za ta shirya a ranar sha tara ga watan Khurdad na shekara ta Hijira Shamsiya a garin Liyon na Faransa.Wannan taro dai zai taimaka matuka gaya wajen bayyana yadda ya kamata a yi rayuwa tsakanin mata da maza rayuwa irin ta Musulunci mai cike da alfano da koyarwa ta dukan bangarori na rayuwa tare da kare hakkokin juna.
579229