Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna bayan ta nakalto daga Isesco hukumar da ke kula da harkokin ilimi d atarbiya da al'adu na Musulunci ta watsa rahoton cewa; hukumar da ke kula da harkokin ilimi da al'adun Musulunci Esesko a daidai lokacin zagayowar ranar sha biyar ga watan Mayu day a yi daidai da ranar iyali ta duniya ta fitar da bayani kan yadda ya zama wajibi a karfafa abubuwa na Musulunci dab a su muhimmanci a tsakanin iyalai. A cikin wannan bayani an yi bayani dalla-dalla kan yadda addinin Musulunci ke girma iyali da ba su matsayi da yanci da girmamawa.
579338