Bangaren kasa da kasa; Limamin Juma'a a Karbala'a a gaban dubban masallata a haramin Imam Huseini (AS) ya nuna damuwa da bacin rai kan yadda ayyukan ta'addanci ke karuwa a kasar Iraki inda ya bukaci samar da hanya ta gaskiya kuma ta hakika da zai kawo karshen kisan gilla ga jama'a.