IQNA

Kungiyar Kasashen Musulmi Ta Nuna A Aikace Na Fuskantar HKI

14:09 - May 19, 2010
Lambar Labari: 1925214
Bangaren siyasa : jagoran juyin juya halin Musulunci a Iran a ranar lirin da marece ne ashirin da bakwai ga watan Ordebehesht na wannan shekara a lokacin da yake ganawa da Abdul Aziz Butafilika shugaban kasar Aljeriya da tawagare da ke mara masa baya ya bayyana karara cewa: kungiyar hadin kan kasashen musulmi dole ta nuna a aikace da gaske take yi wajen fuskantar gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila.



Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan Jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna bayan ta nakalto daga majiyar bada labari ta ofishin jagoran juyin juya halin Musulunci a Iran Hadarat Ayatullahi Khamna'I ta watsa rahoton cewa; jagoran juyin juya halin Musulunci a Iran a ranar lirin da marece ne ashirin da bakwai ga watan Ordebehesht na wannan shekara a lokacin da yake ganawa da Abdul Aziz Butafilika shugaban kasar Aljeriya da tawagare da ke mara masa baya ya bayyana karara cewa: kungiyar hadin kan kasashen musulmi dole ta nuna a aikace da gaske take yi wajen fuskantar gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila. Da dama daga cikin jagorori da shugabannin kasashen musulmi da kungiyoyi da cibiyin musulmi na kiran kungiyar hadin kan kasashen musulmi da shugabannin kasashen musulmi da su yunkuira da fitowa fili wajen kawo karshen makirci da wuce gonad a irin gwamnatin HKI kan al'ummar Palsdinu.


580809

captcha