Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna bayan ta nakalto daga Dunya Bulteni ta watsa rahoton cewa; ministan da ke bawa gwamnatin Turkiya shawara ne a wani zama na ministocin harkokin wajen kasashen musulmi a Tajikistan ya bayyana niyar kasarsa ta gudanar da taron kungiyar hadin kan kasashen musulmi a birnin Akara a shekara ta dubu biyu da goma sha hudu.Cevdet Yilmaz shi ne da kansa ya bada labarin yadda suka tattauna da sauran takwarorinsa na kasashen musulmi kan gudanar da taron wannan kungiya ta hada kan kasashen musulmi a shekara ta dubu biyu da goma sha hudu miladiya a kasar Turkiya.
581765